Singapore ya fi kowane birni tsada

Birnin Singapore Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Birnin na kuma takama da dogayen gine-gine na kawa

Wani bincike da masana tattalin arziki suka yi ya nuna cewa, Singapore shi ne birnin da ya fi kowanne tsadar rayuwa a shekarar 2014.

Darajar kudin kasar da yawan kudin da ake kashe wa wajen kula da mota, bugu da kari da kudaden da ake biya na wutar lantarki da ruwa da sauransu ya sa Singapore ya maye gurbin Tokyo.

Birane biyar dake biye su ne Paris da Oslo da Zurich da kuma Sydney.

A dayan bangaren kuma biranen India na cikin wadanda ba su da tsadar rayuwa a duniya.