Kerry ya soki Rasha game da Ukraine

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya yi tir da abinda ya bayyana a matsayin wata barazana da Ukraine ke fuskanta daga Rasha.

Ya ce ya yi matukar sha'awar juriyar da sabuwar gwamnatin Ukraine ta nuna, wadda ya kira cibiyar da ta fi wakiltar al'umar kasar.

Da yake magana a Kiev, Mr Kerry ya ce bayanin gwamnatin Rasha cewar tana kare masu magana da harshen Rashanci a Crimea ba dalili ba ne, kuma ya zargi fadar shugaban Rashan ta Kremlin da boye hannunta a bayan musgunawa da kuma karya.

Jim kadan kuma shugaba Obama ya nanata abunda John Kerry din ya fada, wanda ya ce gaskiyar cewar sojin Rasha na a Crimea na nufin Rasha na amfani da karfi ba bisa ka'ida ba.

Tun farko dai shugaba Vladimir Putin ya bayyana tsoma bakin kasarsa a Ukraine a matsayin wani aikin jin kai.

Ya musanta cewar dakarun da suka zagayen sansanonin sojin Ukraine a Crimea na da alaka da fadar Shugaban Rasha ta Kremlin.

Mr Putin ya ce dakarun tsaron kai ne na yankin, kuma Rasha ba ta da hannu wajen horar da su.

Karin bayani