Amurka ta zayyana wasu matakai da zasu warware rikicin Ukraine

Shugaba Obama da Vladimir Putin Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Obama da Vladimir Putin

Shugaba Obama na Amurka ya zayyana shawarwarin da yake gani za a iya amfani da su wajen warware rikicin Ukraine.

Shawarwarin sun hada da tura masu sanya ido na kasashen duniya da kuma tattaunawa ta kai tsaye tsakanin Rasha da sabuwar gwamnatin Ukraine.

Mr Obama ya tattauna kan shawarar hakan ne, lokacin ganawarsa ta waya da shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel.

Bisa tsarin na Obama, masu sanya idon za su yi kokarin kare 'yancin 'yan kabilar Rasha da ke Crimea, yayin da ita kuma Rasha za ta saka hakan ta hanyar mayar da sojojinta sansanoninsu.

Ana ganin kila a duba wannan shawara a bayan fagen wani taro da za a yi a Faransa nan gaba a yau, wanda zai hadakan wakilai daga Amurka da Rasha da wasu inda za su tattauna batun Lebanon.