An soki yunkurin halalta tabar wiwi a Uruguay

Wasu masu shan miyagun kwayoyi a Pakistan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasu masu shan miyagun kwayoyi a Pakistan

Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta Majalisar Dinkin Duniya, ta soki wani yunkuri na halatta tabar wiwi a Uruguay da kuma wasu jihohin Amurka.

Hukumar yaki da miyagun kwayoyin ta duniya ta ce shirin ya saba wa 'yarjejeniyar Majalisar da ta takaita amfani da kwayoyi a matsayin na magani da kuma binciken kimiya.

Shugaban hukumar, Raymond Yans ya ce duk wani mataki na sassauta dokokin tabar wiwi zai kasance da hadari ga lafiyar jama'a.

A cikin rahotanta na baya -bayan nan game da halayyar yin amfani da miyagun kwayoyi barkatai, hukumar ta kuma gano karuwa mai yawa a fataucin miyagun kwayoyi a yankin gabashin Afrika, wanda ta ce watakila ma ya kasance cibiya mafi girma a Afrika ga hodar heroin din da ake fataucinta zuwa turai.

Karin bayani