Dubban mutane sun yi zanga zanga a Venezuela

Hakkin mallakar hoto AFP

Dubban masu zanga zanga sun yi tattaki a titunan babban birnin Venezuela, Caracas, inda suke rera wakokin Alla-wadai da gwamnatin gurguzu ta Nicolas Maduro.

Masu zanga zangar na kuma bukatar da a saki tarin mutanen da aka tsare tun lokacin da aka fara zanga zangar wata daya da ya wuce.

Zaman dar -dar na karuwa a Venezuelan yayin da ake shirin gangamin shekara daya da mutuwar tohon shugaban kasar Hugo Chavez, yau Laraba.

Gwamnati ta shirya bukukuwa da dama domin tunawa da ranar, amma kuma masu zanga zangar adawada ita sun lashi takobin komawa bakin zanga zangarsu.