Abacha: Amurka ta ƙwace naira biliyan 76

Hakkin mallakar hoto nigeria at 50
Image caption Ana zargin marigayi janar Sani Abacha da satar makudan kudade mallakar Nigeria lokacin mulkinsa.

Amurka ta ce tana ƙwace da fiye da dalar Amurka 450 miliyan, wato daidai da naira biliyan 76.5 mallakar tsohon shugaban kasar Najeriya, Sani Abacha da abokan burminsa.

Ma'aikatar shari'ar Amurka ta ce wannan ne adadin kudi mafi girma da ta taba kamawa da ya shafi rashawar jami'an kasashen ketare.

Ma'aikatar ta ce kudaden da aka boye a asusun bankuna da ke Birtaniya, Jersey da Faransa, an same su ne ta hanyar rashawa da cuwa-cuwa, a zamanin da marigayi Janar Abacha ke mulkin soji a Najeriya.

Janar Abacha ya mulki kasar ne daga 1993 zuwa mutuwarsa a 1998, ana tsaka da shirye-shiryen zarcewarsa kan mulki a matsayin farar hula.

Karin bayani