'A riƙa jin kan dabbobi kafin a yanka su'

Hakkin mallakar hoto AFP

Wani babban jami'in kiwon lafiyar dabbobi a Birtaniya ya bukaci a sanya ɗan jin ƙai a yadda aka yanka dabbobi bisa koyarwar wasu addinai.

John Blackwell na kungiyar likitocin dabbobi ta Birtaniya ya ce, domin ragewa dabbobi irin azabar da suke sha yayin yanka kamata yayi a fitar da su daga hayyacinsu sosai kafin a yi musu yanka bisa koyarwar Musulmi da Yahudawa.

Ya kuma ce, idan har hakan ba za ta yiwu ba, to kamata yayi a rubuta a jikin naman a fili cewa, ga hanyar da aka yi yankan.

John Blackwell ya ce, idan har hakan ba zata samu ba to kamata ya yi ma a haramta yanka dabobbi ta hanyar da Musulmi da Yahudawa suke yi.

Bara ne dai kasar Poland ta haramta yanka dabbobi kamar yadda Musulmi da Yahudawa suke yi.