Jiragen Attajiran Najeriya

Wani jirgi mallakar wani mai kudi a Najeriya

Kauce wa zirga-zirga a jiragen fasinja na 'yan kasuwa, ya sa masu hannu da shuni dake sayen jiragen sama na karuwa a Najeriya.

Wasu Injiniyoyi na aiki a kan wasu jirage a jere dake sheki.

Peter de Waal, wani jami'i ne a kamfanin ExecuJet Aviation Nigeria, dake ajiye jirage tare da kulawa da su kuma ya ce "Akalla akwai jiragen sama guda tara na mutane a wajen ajiyar jiragen saman nan."

"Ana kulawa da jirage a Turai da Amurka, amma ayyukanmu a nan na taimaka wa ta bangaren kudin da za a kashe da kuma lokaci." De Waal ya shaida wa BBC.

Matafiya a jiragen sama na 'yan kasuwa, ko da kuwa a kujera mai matsakaicin kudi ne, akwai matsaloli tattare da su kamar samun jinkiri da sauya wajen sauka,abin da ke janyo rashin jin dadi ga kowa, ciki har da wadanda bata lokaci zai iya janyo musu asarar kudi.

Rady Fahmy wani jami'i ne a kungiyar 'yan kasuwa masu zirga-zirga a jiragen sama "Da wuya ace ga yawan jiragen sama mallakar daidaikun mutane a Najeriya, saboda mafi yawansu an yi rajistarsu ne a kasashen waje."

Image caption Haka ma yawan masu shatar jirage na karuwa a Najeriya

"Maza da mata 'yan kasuwa sun mallaki jiragen sama a Najeriya da ma Afrika." Inji Rady.

Yawancin masu jirage basa son a san suna da shi, amma a tsakanin masu kudin sun san abin da suka mallaka.

Hamshakan masu kudi sun fi son Jirgin sama Bombardier Global Express XRS, da ya kai kudi dala miliyan 50.

Cikinsu har da Aliko Dangote, da hamshakiyar mai hada-hadar mai Folorunsho Alakija da Mike Adenuga mai kamfanin waya, wadanda sun mallaki kanana da manyan jiragen sama.

Image caption Masu jiragen na kawata su yadda suke so

Wasu jiragen saman da 'yan siyasa da malaman addinin kirista suka mallaka sun hada da Gulfstream G550 da Bombardier challenger 605 da Dassault Falcon 900 da kudadensu ya kama daga dala miliyan 57 zuwa 39.

Najeriya na samun habakar tattalin arziki, sai dai abin da mutane da dama ke cewa shi ne, kalilan ne ke gani a kasa.

Kuma a shekarar 2013, hukumar kula da zirga-zirgan jiragen sama ta Najeriya ta sanya harajin dala 3000 ga dukkan jirgi mallakar daidaikun mutane, a duk lokacin da za su tashi, amma majalisar dattawan ta dakatar da harajin.

Abin da ke nuna cewa mata da maza 'yan kasuwa na da karfin fada aji a siyasar kasar.