Sanatoci za su jajirce kan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hare haren sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da asarar dukiya da dama a cikin kwanakin nan.

'Yan majalisar dattawan Najeriya, musamman na arewa maso gabashin kasar, za su gabatar da wani kuduri mai karfin gaske da zai taimaka wajen kawo karshen hare-haren da ake kaiwa a yankin.

A cikin kwanakin nan dai an kona kauyuka an kuma kashe mutane da dama a jihar Borno a hare-haren da ake dangantawa da kungiyar da ake kira Boko Haram.

Sanata Ahmad Zannah na cikin 'yan majalisar dattawan da suka fito daga jihar ta Borno, wadanda suka lashi takobin daukara wannan mataki na gabatar da kudurin.

Karin bayani