Borno: Akwai matsalar kai kayan agaji

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Mutane da dama a jihar Borno sun gudu daga ƙauyukansu

Hukumar bada agajin gaggawa ta Nigeria NEMA ta ce, tana fuskantar matsala wajen kai kayan agaji zuwa kauyukan jihar Borno inda 'yan Boko Haram suka kai harin da ya halaka mutane da dama.

Babban jami'in hukumar mai kula da yankin arewa maso gabas, Muhammed Kanar ya ce, da zarar sun tunkari wasu kauyuka domin kai kayan agaji sai mutane su soma guduwa saboda tsoron cewa, ko wani sabon harin za a kai musu.

Yanzu haka dai mazauna kauyuka da dama a jihar Borno suna cikin mawuyacin hali saboda firgicin hare-haren da aka kaiwa kauyuka kamar Jakana da kuma Mainok, inda aka kashe jama'a da dama.

Wani mazaunin garin Magumeri ya fadawa BBC cewa, mutane suna cikin firgici saboda rashin tabbas akan abinda zai iya faruwa da su kowanne lokaci.

Mazauna kauyukan jihar Borno da dama ne suka tsere saboda fargaba bayan hare-haren da aka kai Mainok da Jakana.