Shekara guda bayan mutuwar Chavez

Hakkin mallakar hoto v

A Caracas babban birnin Venezuela an yi wani babban gangami na tunawa da marigayi shugaba Hugo Chavez wanda ya rasu shekara guda kenan da ta gabata.

Dubban dakakarun kasar da kuma masu goyon bayansa ne suka yi wani maci.

Wanda ya gaje shi, wato shugaba Nicolas Maduro ya yi jawabin yabawa marigayin.

An yi wannan gangami ne bayan an shafe makonni ana boren da ya wanzar da zaman dar-dar a kasar.

Sai dai kuma koda shugabannin 'yan adawa sun bukaci magoya bayansu su girmama wannan rana.

Amma duk da haka wasu masu goyon bayan 'yan adawa sun ce, zasu cigaba da kasancewa a inda suka yi zaman dirshan.

Mutane 18 ne suka mutu tun daga lokacin da aka soma bore a Venezuela.