Nigeria: 'Ana samun nasara akan 'yan Boko Haram'

Hakkin mallakar hoto Reuters

A Najeriya rundunar Sojin saman kasar ta ce ta na samun nasara a yakin da take yi da 'yan Kungiyar nan da ake cewa Boko Haram yayin da ta yi ikirarin ci gaba da kaddamar da hare hare ta sama a wasu sansanonin 'yan kungiyar a arewa maso gabashin Nigeria.

Kakakin rundunar sojan saman Nijeriya, Air Commodore Yusuf Anas ya fadawa BBC cewa, yanzu an samu fahimtar juna sosai tsakanin rundunonin sojan, kuma suna aiki tare wajen kawo karshen hare-haren kungiyar Boko Haram.

Rudunar sojan saman Nijeiryar ta kuma ce, tana samun nasara a yaki da 'yan Boko Haram saboda tsaron tsarin da ake amfani da shi wajen yin yakin.

Sun ce, yanzu sun samu nasarar tarwatsa 'yan Boko Haram daga wuraren da suka buya, dan haka ne ma suka bazama suke kaiwa kayuka hare-hare.