Nigeria: An kashe mutane 18 a Benue

Hakkin mallakar hoto AFP

A jihar Benue ta Nigeria, an kashe mutane aƙalla18 yayin hari a kauyuka hudu, da suka hada da Anyiase, da Moon da, Waya da kuma Ihyundugh.

Mazauna ƙauyukan sun zargi makiyaya Fulani da aikata kisan a garuruwan da 'yan ƙabilar Tiv ne suka fi yawa.

Sai dai kuma shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah a jihar Benue, Alhaji Haruna Garba Gololo, ya musanta hannun Fulani makiyaya a harin na kauyukan hudu.

Alhaji Haruna Gololo ya kuma ce, wasu da ake zaton yan ƙabilar Tiv ne sun kai hari a Kashim Bila, wanda ƙauyen Fulani ne inda suka kashe mutane biyar kana suka yi awon gaba da shanu.

Ƙauyukan da aka kai wadannan hare-hare da asubahin yau suna kan iyakar Nigeria da Kamaru inda aka ce makamai sun yi yawa a hannun jama'a

An jima ana fama da rikici tsakanin Fulani makiyaya da 'yan kabilar Tivi.