Karya ta yi tafiyar mil 12 a injin mota

Karya mai suna Betty Boop
Image caption Betty Boop wata karya a Manchester

Wata karya ta auna arziki, bayan an yi tafiya da ita na mil 12 tana makale a cikin injin mota.

Karyar mai suna Betty Boop 'yar wata uku a duniya, ta shiga cikin injin motar ne a garin Manchester dake Birtaniya.

Kuma bata ji ko da kwarzane ba, bayan an yi gudu da ita, makale a injin mota a yankin Salford na Manchester.