Sudan ta Kudu: An kashe soja 5

Hakkin mallakar hoto AFP

An tabbatar da mutuwar soja biyar a Sudan ta kudu yayin da fada ya barke a cikin babban barikin soja dake Juba, babban birnin kasar.

Wani kakakin soja ya ce, wau mutanen uku sun jikkata yayin da hayaniya ta barke a wurin biyan albashin soja, saboda jinkirin da aka samu wajen biyan albashin.

An shafe sa'a guda ana musayar wuta, lamarin da ya sa mutane da dama suke rika gudu da gidajensu.

Tashin hankalin da ake yi a Sudan ta kudu tun daga watan Disamba ya samo asali ne daga rashin jituwa tsakanin shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa, Riek Machar.

Tun daga wancan lokacin zuwa yanzu mutane da dama ne aka kashe a sassa da dama na kasar.