Tunisia: An saki wanda ya ci zarafin addini

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban 'yan Salafiyya na Tunisia na cikin masu adawa da sakin mutumin

An saki wani mutum dan Tunisia da aka yanke wa zaman gidan yari saboda laifin sanya hoton barkwanci na Manzon Allah annabi Muhammad (SAW ), a shafin sada zumunta na Facebook.

An saki mutumin ne me suna Jabeur Mejri bayan ya yi shekaru biyu daga cikin bakwai da rabi na hukuncin da aka yanke masa, sakamakon afuwar shugaban kasar.

Masu rajin kare hakkin dan adam, a kasar ta Tunisia, sun bayyana sakin mutumin da cewa nasara ce ga dukkanin masu rajin tabbatar da 'yancin tunani da bayyana ra'ayi.