Crimea ta kada kuri'ar hade wa da Rasha

Majalisar dokokin Crimea Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Majalisar dokokin Crimea

'Yan majalisar dokokin yankin Crimea sun kada kuri'a da gagarumin rinjaye, na amince wa yankin ya zama bangaren Rasha.

Za kuma a gudanar da kuri'ar raba gardama akan shirin nan da kwanaki goma, lokacin da akasarin al'ummar kasar masu amfani da harshen Rashanci za su iya amince wa da shi.

Mataimakin kakakin majalisar dokokin Crimea, Sergei Shuvainikov ya shaida wa manema labarai a Simferopol cewa, abubuwa biyu za'a tambaya a takardar kuri'ar.

"Ta farko kun amince da a hade da yankin Crimea da tarayyar Rasha, ta biyu kuma kun amince da a maido da tsarin mulki na 1002 kuma Crimea ta zamo bangare na Ukraine."