Facebook ya dauki matakai kan bindiga

Image caption Facebook ya ce ya tattauna da masu ruwa da tsaki kafin sanya tsauraran dokokin a kan bindiga

Dandalin sada zumuntan da ya fi kowanne girma a duniya, Facebook ya tsaurara matakai a kan batutuwan da suka shafi bindiga.

Shafin ya ce zai cire duk wani batu da masu amfani da shi suka rubuta na karya dokar da ta shafi sayar da bindiga.

Haka kuma zai hana wadanda shekarunsu ba su kai sha takwas ba, ganin duk wani abin da aka wallafa a shafin da ya shafi bindiga da ma wasu kayayyakin da aka takaita ko hana amfani da su.

Ko da yake shafin ba na tallace-tallace ba ne, amma mutane kan yi amfani da shafin na Facebook wajen tallata hajar da aka sanya wa dokoki ko masu janyo kace-nace.

Dandalin dai ya fuskanci matsin lamba daga kungiyoyi, domin ya sauya dokokinsa da suka shafi batun sayar da bindigogi.

Facebook ya ce "Mutane sun nuna damuwa game da yadda ake tallar bindigogi a shafin."

Sabbin dokokin Facebook din da za su fara aiki a makonni masu zuwa, za kuma su shafi bangaren hoto wato Instagram.