Mata sun yi zanga-zanga a Lagos

Taswirar Najeriya
Image caption Ana zargin kungiyar Boko Haram da kai hare-haren baya-bayan nan, a arewa maso gabashin Najeriya

Wasu mata sun yi zanga-zanga a Lagas, domin nuna bacin ransu game ci gaba da kashe-kashen mutane da ake fama da shi a arewa-maso-gabashin Najeriya.

Matan wadanda yawansu ya haura dari sun je fadar gwamnatin jihar, inda suka mika kokensu game da zubar da jinin da ke faruwa a jihohin Borno, Yobe, Adamawa da kuma Pilato, suna neman gwamnatin tarayya ta kawo karshen hakan.

Daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu a 'yan kwanakin nan a wadannan jihohin, ko da yake gwamnatin kasar na ikirarin shawo kan matsalar.

Dubban mutane ke cikin halin tagayyara mafi yawansu mata da kananan yara.