'Saadi ya sabawa sharuddan mafakar da mu ka ba shi'

Hakkin mallakar hoto Reuters

Gwamnatin Jumhuriyar Nijar ta tabbatar cewa ita ce ta mika dan tsohon jagoran Libya, Moammar Gaddafi, watau Saadi Gaddafi ga hukumomin Libya.

A lokacin wani taron manema labarai da ya kira yammacin Alhamis a Yamai, kakakin gwamnatin Nijar din, Malam Marou Amadou, ya ce gwamnati ta tesa keyar Saadi Gaddafin ne saboda ya saba wa sharuddan da gwamnatin ta shinfida ma shi a lokacin da ta ba shi mafaka a shekara ta 2011.

Malam Marou Amadou, ya ce sun gaano cewa akwai wani na kusa da Saadi Gaddafin da ya rika zuwa kudancin Libya mai fama da rikici ya kuma dawo birnin Yamai, ba tare da sanin hukumomin Nijar din ba.

Kakakin gwamnatin Nijar din ya ce ba za su yarda ba wasu mutane su yi zagon kasa ga hukumomin Libya daga cikin Nijar ba saboda a cewarsa burin gwamnatin Nijar shi ne ganin an samu kyautatuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Ana zarginsa da kashe masu zanga zanga da kuma wasu laifuka a lokacin mulkin mahaifinsa

A baya dai Niger taki amincewa da bukatar mika shi.

Karin bayani