Shirin gudanar da kuri'ar rabagardama a Crimea

Shugaban rikon Ukraine,  Oleksander Turchinov Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Turchinov ya ce shirin kuri'ar raba gardamar haramtacce ne

Shugaban rikon kwaryar Ukraine Oleksander ya ce kuri'ar raba gardamar da majalisar dokoki Crimea mai goyon bayan Rasha ta shirya haramtacciya ce.

Firaministan rikon kwaryar Ukraine Arseniy Yatsenyuk ya shaidawa manema labarai cewa a Brussels cewa, gwamnatin Ukraine ce kadai ke da damar yanke shawara akan makomar Crimea.

A waje daya kuma, a gabashin Ukraine, sojojin kasar sun tsare jagoran kungiyar da ke marawa gwamnatin Rasha baya a birnin Donestk wato Pavel Gubarev.

A 'yan kwanakin nan, an samu gwabzawa a birnin na Donestk tsakanin masu zanga-zangar da ke marawa gwamnatin Rasha baya da kuma wadanda ke adawa da gwamnatin.

A halin da ake ciki kuma, shugaban kasar Amurka Barrack Obama ya gargadi Rasha akan Ukraine, inda ya hakikance cewa, Amurka da kawayenta sun kuduri aniyar yin adawa da duk wani mataki da ya saba da dokokin kasashen duniya.

Karin bayani