Kotun duniya ta yanke wa Katanga hukunci

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya dake birnin Hague ta yanke wa madugun sojan sa kai na Congo, Germain Katanga hukuncin laifukan yaƙi da kuma cin zarafin bil'adama.

Kotun ta samu Germain Katanga ne da laifin kitsa kashe mutane yayin hare-hare a wani kauye dake gabashin jamhuriyar dimukradiyyar Congo cikin shekara ta 2003.

Amma an wanke shi daga zargin aikata fyade da cin zarafin mata da amfani da yara kanana a matsayin soja.

Wannan shari'a ta Katanga ta sha banban da kowacce saboda an same shi ne da laifi dangane da hari daya.

Germain Katanga shi ne mutum na biyu da kotun ta duniya ta yankewa hukunci tun bayan kafa ta shekaru goma sha biyu da suka wuce.