APC ba ta miƙa wakilan taron ƙasa ba

Jam'iyyar adawa ta Nijeriya APC ba ta miƙa sunayen wakilanta da zasu halarci taron kasa da gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta shirya.

Jiya ne dai aka fidda sunayen wakilan da zasu halarci taron, amma jerin sunayen ya nuna jam'iyyar adawa ta APC ba ta mika wakilai ba.

Tun farko dai shugabannin jam'iyyar adawar ta APC sun soki taron kasar, suna cewa, wata hanya ce kawai ta kawar da hankalin 'yan Nijeriya daga muhimman abubuwa.

Wakilai 492 ne baki daya zasu zauna a taron kasa, kamar yadda sanarwar da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin Najeriya ta ce.

Kashin dattawa sun hada da mutane irinsu Cif Edwin Clark da Cif Olu Falae da Farfesa Jerry Gana da Malam Tanko Yakasai da Farfesa jibril Aminu.

Akwai kuma kashin jami'an tsaro da su kayi ritaya da suka hada da janar Zamani Lekot da Alhaji Bashir Albasu da Alhaji Mamman Misau.