An karbe garin Hudur a hannun Al Shabaab

'Yan kungiyar Al Shabaab Hakkin mallakar hoto
Image caption Al Shabaab ce ke da iko da yawancin kudanci da tsakiyar Somaliya

Jami'ai a Somaliya sun ce dakarun kasar da na Habasha, sun kwace garin Hudur daga hannun kungiyar masu fafutukar Islama ta Al Shabaab.

An yi artabu a wajen garin, wanda shi ne babban birnin yankin kudu-maso yammacin Bakol, kafin Al Shabaab ta janye.

A ranar Alhamis ne dakarun Habasha suka kwace gundumar Radbure, wanda shi ma ke cikin yankin na Bakol.

Sai dai mazauna yankin sun ce 'yan kungiyar ta Al Shabaab sun dawo gundumar, bayan wasu 'yan sa'oi.

A 'yan makonnin na dai gwamnatin Somalia ta sha amabata cewa za ta kai hare-hare kan Al Shabaab.