Za a 'haramta' Facebook a Turkiyya

Image caption Recep Tayyip Erdogan, firaministan Turkiyya

Firaministan Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya ce, gwamnati zata iya haramta amfani da shafukan sada zumunta kamar Facebook da kuma shafin YouTube mai watsa hotunan vidiyo.

Recep Erdogan ya ce, wadannan shafuka na sada zumunta suna yin barazana ga gwamnatinsa.

A irin wadannan shafuka ne ake ta nanata zargin aikata cin hanci da rashawa da ake yiwa Recep Erdogan.

Zarge-zargen sun hada da wanda ya fito cikin makon jiya inda aka yada maganganun firaminstan ta waya, yana fadawa ɗan sa yadda za a ɓoye wasu maƙuden kuɗaɗe.

Erdogan ya ce, ƙage aka yi masa, aka yaɗa a shafukan sada zumunta, kuma aiki ne na makiyansa.