An kai wa gidan gwamnatin Enugu hari

Hakkin mallakar hoto

An kashe akalla mutum daya a wani harin da wasu matasa su ka kai wa gidan gwamnatin Jihar Enugu a kudu-maso-gabacin Najeriya.

Rundunar 'yan sanda a jihar ta ce an kai harin ne ran Asabar din nan da safe.

Ta ce ta na gudanar da bincike game da harin, wanda ta ce matasa ne su ka kai shi.

Sai dai ba a kai ga samun cikakken bayani game da maharan da manufarsu ta kai harin ba.

Amma wani mai magana da yawun gwamnan jihar Enugun ya ce an cafke ukku daga cikinsu.

Karin bayani