Wammako: 'Jonathan na yawon gantali'

Hakkin mallakar hoto sokoto govt
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan ya kai ziyara fadar Sarkin Musulmi

Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi Allah wadai da wata ziyara da shugaban kasar Goodluck jonathan ya kai jiharsa ranar Asabar.

Gwamnan ya ce bai dace shugaban kasar ya shagaltu da ziyarce-ziyarcen wasu wurare saboda lamuransa na siyasa ba, alhali bai taka kafarsa a jihohin uku na arewa maso gabashin kasar inda ake ci gaba da hasarar daruruwan rayuka sakamakon hare-haren masu tayar da kayar baya.

A ranar Asabar ne dai Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya kai ziyara Sokkoto inda yaje fadar Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar.

A baya ma dai jam'iyyun adawa sun zargin Shugaban Kasar da yawace yawacen ziyara zuwa sarakunan gargajiya domin cimma manufar sa ta siyasa.

Sai dai fadar Shugaban Kasar ta yi watsi da wannan zargi tana mai cewa ziyara ce ta girmama Sarakunan.