Ana neman jirgin Malaysia da ya bace

Hakkin mallakar hoto Reuters

Masu aikin ceto na kasa-da-kasa na ci gaba da neman wani jirgin Malaysia da ya bace.

Sun maida hankali ne akan wani yankin teku dake tsakanin Malaysian da Vietnam.

Rundunar sojin Malaysian ta ce ta sake tura wata tawagar helikoftoci da jiragen ruwa, amma dai har yanzu basu ga alamar komi ba.

Jirgin dai, samfurin Boeing 777, na dauke ne da fasijoji 239 da kuma matukansa.

Jami'an kamfanin safara jiragen Malaysian sun ce ba su samu sakonni damuwa daga jirgin ba bayan barinsa birnin Kuala Lumpur.

Sun ce jirgin na dauke ne da fasinjoji daga kasashe 14, wadanda yawancinsu 'yan kasar China ne.

Ministan sufurin Malaysian, Hishammuddin Hussein, ya ce su na kokarin bayar da dukkan bayanan da suka samu ga jama'a cikin hanzari.

Firaministan kasar, Najib Razak, ya ce sojin ruwan Amurka na taimakawa wajen bincike.

Yace: "Ta hanyar sojin ruwa, Amurka ta amince ta sanya jiragenta su taimake mu wajen bincike da aikin ceto. Muna ta kokari muna bin sahun duk ta inda jirgin yabi".

Tun da farko dai shugaban kamfanin safarar jirage a Malaysian, Ahmad Jauhari Yahya, ya ce suna tuntubar 'yan uwan fasijojin domin nuna damuwarsu.

Yace: "Mun dukufa ne a yanzu wajen aikin kwana-kwana; kuma hukumomi na ba da cikakken tallafi. Tunanen mu da addu'o'inmu na ga fasinjoji da matukan jirgin da iyalansu".

Irin wannan samfurin jirgin dai bai cika samun matsala ba tunda aka fara amfani dashi shekaru 19 da suka gabata. Babban hadarin da aka samu dashi shine a bara, inda mutane ukku suka mutu a San Fransisco a Amurka.

Shi kuwa kamfanin safarar jiragen sama a Malaysian ya ga hadari mafi muni ne a shekarar 1977, lokacin da kusan mutane 100 su ka mutu a wani jirgin da ya fadi a kasar.

Karin bayani