Jirgi ya bace daga Malaysia zuwa Beijing

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jirgin na dauke da mutane sama da 200

Wani jirgin saman Malaysia dauke da fasinjoji 239 ya bace sa'o'i kadan bayan tashi daga Kuala Lumpur a kan hanyarsa ta zuwa Beijing.

Kamfanin dillancin labaran gwamnatin China ya ce jirgin kirar Boeing 777 na sararin samaniyar Vietnam ne lokacin da na'urorin sadarwar filayen jiragen sama su ka daina ganinsa.

Kakakin kamfanin jirgin ya ce mahukuntan Malaysia da Vietnam na laluben jirgin a yankin tekun kudancin China.

Akwai dai 'yan kasashe 14 a cikin jirgin

'Ya fada cikin teku'

Kafafen yada labaran gwamnatin Vietnam sun ce wani sojan ruwa ya tabbatar da cewa jirgin sama Malaysia dauke da mutane dari biyu da talatin da tara ya fada teku daf da gabar kasar.

Jirgin ya bace ne sa'o'i biyu bayan tashi daga Kuala Lumpur a kan hanyarsa ta zuwa Beijing, inda na'urorin sadarwa na tashoshin jiragen sama su ka daina ganinsa.

Sai dai babu wani cikakken bayani game da wannan rahoto daga bangaren Malaysia da kuma Beijing.