Fasfon sata ya janyo shakku ga bacewar jirgi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Biyu daga cikin pasinjojin jirgin na dauke na fasfo na sata

Hukumomi a Malaysia sun ce su na bincike game da fasinjoji hudu da ke cikin jirgin saman kasar da ya bace a tekun kudancin China ranar Asabar.

Akalla biyu daga cikin fasinjojin dai na amfani ne da fasfo na sata.

Ministan sufuri na Malaysia, Hishamaddin Hussein ya shaida wa manema labarai a Kuala Lumpur cewa hukumar leken asiri da jami'an yaki da ta'addanci na Malaysia na bincike game da fasinjojin.

Kawo yanzu dai masu bincike sun ce da alamu jirgin sama ya juya zuwa Malaysia kafin na'urorin sadarwar tashoshin jiragen sama su daina ganinsa.

Karin bayani