Amurka na son karin jiragen leken asiri a Afirka

  • 8 Maris 2014
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Amurka na da jirage biyu a Jamhuriyar Niger

Rundunar sojojin Amurka ta ce ta na fama da karancin jiragen leken asiri a yankin yammacin Afrika wadanda za su bata damar bin diddigin irin ayyukan ta'adancin da ke faruwa a yankin.

Shugaban rundunar sojin Amurka da ke sa ido a kan nahiyar Afrika Janar David Rodriguez ne ya bayyana hakan a lokacin da ya bayyana a gaban majalisar dokokin kasar.

Janar David ya ce a yanzu jiragen da suke da su sun yi kadan, kasancewar a kasashen da ke yammacin Afrika akwai inda ake fama da rikicin masu tada kayar baya musamman a yankin Sahel.

Ya kuma ce a yanzu suna matukar bukatar wadannan jirage domin barazanar tsaro da suke fuskanta a yammacin Afirka

Amurka dai nada jirage a Jamhuriyar Niger kuma masu lura da al'amuran siyasa na ganin cewa zata iya neman amfani da irin wadannan jirage watarana a Kasashen dake makwabtaka da Niger din kamar Nigeria.