Tulin shara na neman mamaye birnin Rio de Janeiro

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tulin sharar bikin raye raye na babban birnin Brazil

Sharar da ta taru a Rio de Janeiro babban birnin Brazil tsawon kwanaki hudu da aka kwashe ana bikin raye-raye na Carnival na neman mamaye birnin kasancewar masu sharar tituna na ci gaba da yajin aikinsu na mako guda.

Masu sharar na neman karin albashi ne da kuma inganta tsarin aikinsu, inda a ranar Juma'a suka gudanar da zanga-zanga a harabar ofishin magajin garin Rio.

Yankunan bakin ruwa na Ipanema da Copacabana da suka shahara wurin kyau sun dume da warin bola, yayinda unguwannin talakawan birnin ma ke fama da hamamin sharar.

An dai sa 'yan sanda su kare ma'aikatan sharar da su ba su shiga yajin aikin ba, yayinda mahukunta su ka bukaci magidanta su tara shararsu a cikin gidajensu.