An zargin jam'iyyar kwaminis a China

Jam'iyyar kwaminist ta China Hakkin mallakar hoto
Image caption Jam'iyyar kwaminist ta China

Jami'ai a yankin Hunan a China sun zargi mahukuntan jam'iyyar gurguzu da gana musu azaba domin samun bayanai akan cin hanci.

Mutanen su hudu sun shaidawa kamfanin dilancin labaru da AP cewa sun shafe tsawon watani ana cin zarafinsu ta hanyar hanasu barci da abinci , tare kuma da lakada musu duka.

Mutanen sun ce sun yi magana ne domin suna son sharia ta yi musu adalci.

Sun kuma ce rayuwarsu ta na cikin hadari sakamakon matakin da suka dauka na fitowa fili da bayanansu.

Sai dai jami'an Jam'iyyar kwaminist da kamfanin AP ya tuntuba sun musanta zargin .