An sako matan da ke yiwa coci hidima

Matan da ke yi wa addinin kirista hidima a Syria Hakkin mallakar hoto c
Image caption Matan da ke yi wa addinin kirista hidima a Syri

Yanzu dai an tabbatar da cewa 'yan tawayen Syria sun saki wasu mata masu yiwa addinin kirista hidima da kuma wasu masu yi musu aikatau a gida su uku da suka kama tun shekarar da ta wuce.

Matan su 13 sun sauka q wani gari da ke kan iyaka da Lebanon, bayan tafiyar da suka yi ta sa'oi tara.

Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na Faransa ya ce matan sun gaji ainun , biyu daga cikinsu ma, har takai sai da aka sakko da su daga motarsu.

A watan Disamba ne dai aka sace matan kiristoci daga wurin ibadarsu bayan da 'yan tawaye suka kama wurin.

Wani janar na sojin Lebanon da ya taimaka wajen ganin an sake su, ya ce, gwamnatin Syria, za ta saki fursunoni mata kusan 150 a musaya da su.