'Yan cirani fiye da 40 sun hallaka a tekun Yemen

Wasu 'yan cirani daga nahiyar Afrika Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu 'yan cirani daga nahiyar Afrika

Jami'ai a kasar Yemen sun ce yan cirani fiye da 40 da suka fito daga nahiyar Afrika suka mutu lokacinda da jirgin ruwan da suke ciki ya nutse a gabar tekun Yemen dake kudancin kasar.

Ma'aikatar tsaro ta kasar ta ce wani jirgin ruwa na soji dake sintiri ya ceto mutane akala talatin.

Kungiyar da ke sa ido a kan alamuran 'yan cirani ta duniya ta ce dubban 'yan gudun hijira daga Somalia da kuma Habasha ke bin tekun Aden a kowace shekara.