Tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta isa CAR

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Musulmi da dama sun tsallaka kasar Kamaru

Shugaban tawagar Majalisar Dinkin Duniya dake binciken hargitsin da ya faru a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ya ce yana fatan hana kisan kare dangi.

Mista Bernard Acho Muna ya ce bai kamata kasashen duniya su tsaya har sai ta'asar kisan kare dangi ya auku ba, yace akwai bukatar hukunta masu kalaman haddasa kiyayya.

Ya kara da cewar "Yana daga cikin aikin mu mu gano yadda za mu kawo karshen dukkan wani lamari da zai kai ga kisankare dangi."

Nan gaba a ranar Litinin tawagar za ta isa babban birnin kasar Bangui.

A cikin watan Disamba ne kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya kafa kwamiti don binciken bin zarfin bil adama a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Kusan mutane dubu 650 ne suka rasa muhallinsu sakamakon rikici a kasar.

Karin bayani