Sojin Isra'ila sun bindige dan Jordan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Isra'ila na sintiri a kan iyakokin kasar

Sojojin Isra'ila sun bindige wani alkali dan kasar Jordan a lokacin yana kokarin tsallaka wa zuwa Jordan daga gabar yamma da kogin Jordan.

Jami'an Falasdinawa dana Jordan sun ce mutumin Raed Zeiter haifaffen Falasdinu ne amma yana aikin alkalanci a Jordan.

Hukumomin Israi'la sun ce suna gudanar da bincike kan lamarin.

A cewarsu an harbe shi ne bayan da ya yi kokarin kwace bindigar wani sojin Israi'la a kan iyakar.

Karin bayani