Shugaban Kenya ya rage wa kansa albashi

kenyatta Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Kenyatta da mataimakinsa William Ruto

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya sanar da rage albashinsa da sauran ministoci don rage kudaden da gwamnati ke kashewa kan albashin jami'anta.

Shugaba Kenyatta da mataimakinsa William Ruto za rage musu albashi da kashi 20 cikin 100 a yayinda sauran ministoci za a rage musu albashi da kashi 10 cikin 100.

Mr Kenyatta kuma ya bukaci 'yan majalisar dokokin Kenya wadanda suna daga cikin wadanda suka fi albashi mai tsoka a Afrika suma su amince a rage musu albashi.

Shugaban ya ce gwamnati na kashe kusan $4.6bn wajen biyan albashi a yayinda ya rage $2.3bn wajen gudanar da ayyukan ci gaba kasa.

Karin bayani