INEC ta gargadi 'yan siyasar Nigeria

Farfesa Attahiru Jega
Image caption Farfesa Attahiru Jega shugaban hukumar zabe ta Najeriya

Hukumar zabe ta Najeriya mai zaman kanta, INEC, ta gargadi jam'iyyun siyasar kasar su guji yi wa dokokin zabe da suka jibinci yakin neman zabe karan tsaye.

Hukumar ta ce lokaci bai yi ba da 'yan takara za su fara zawaracin masu zabe, don haka haramun ne a rika shelar takarar a daidai wannan lokaci.

Mista Nick Dazang mai magana ne da yawun hukumar kuma ya ce kusan duk jam'iyyun siyasar kasar sun sabawa doka.

Ya kuma ce dokokin zabe na kasar sun ba hukumar damar hukunta duk wani da ya sabawa doka.