USAID za ta tallafawa Niger da Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dubban mutane sun ci ribar tallafin USAID a Afrika

Hukumar raya kasashe ta Amirka, USAID ta kaddamar da wani shirin yaki da talauci a kasashen Nijar da Burkina Faso.

Hukumar ta ce ta ware kimanin dala miliyan 70 na Amirka, domin tallafa wa mutanen da ke fama da karancin abinci a kasashen biyu.

A karkashin shirin, wanda ake yiwa lakabi da RICE, jumhuriyar Nijar za ta samu dala miliyan 45 ne, kuma za a gudanar da shirin ne a jihohin Tillabery da Maradi da kuma Damagaram.

Shugaban Hukumar nan da ake yiwa lakabi da 3N, watau 'yan Nijar su ciyar da Nijar, Dr Amadou Alahouri, ya shaidawa BBC cewa manufar shirin, wanda zaa kwashe shekaru biyar ana aiwatarwa, ita ce bunkasa harkar noma da kiwo a jihohin uku.

Shirin na RICE dai yana a matsayin wani bangare ne na tsarin da Amurka ta bullo da shi na tallafawa kasashe 9 na yankin Sahel wajen yaki da matsalar karancin abincin da miliyoyin jamaa ke fama da ita a yankin.

Tsarin yana da burin rage yawan kananan yara masu fama da tamowa a Nijar daga kashi 15 daga cikin 100 a yanzu zuwa kasashi 10 daga cikin 100.

Karin bayani