Mutane biyar sun mutu a rikicin Benue

taswirar Nigeria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kimanin shekaru uku kenan ana samun rikici tsakanin Tiv da Fulani a Benue

Rahotanni daga jihar Benue da ke arewa-maso-tsakiyar Najeriya na cewa, akalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu a karamar hukumar Guma da ke jihar.

Sakamakon wani hari da aka kaiwa kauyuka kusan 20 a yankin, a rikicin da ke da nasaba da tashin hankali tsakanin mazauna yankin da Fulani makiyaya a ranar Talata.

Gwamnan jihar Gabriel Susuwan na wata ziyarar gani da ido a yankin, domin ganin irin barnar da aka yi sakamakon rikicin.

Tashin hankalin ya kai ga kona amfanin gona mai tarin yawa.

Sai dai Fulani makiyaya sun musanta kai hare-haren, inda suka ce sune ma ake sace wa shanu.