Gwamnan jihar Benue ya tsallake rijiya da baya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Najeriya

Rahotanni daga jihar Benue da ke yankin arewa ta tsakiyar Najeriya, sun ce gwamnan jihar, Mista Gabriel Suswam ya tsallake rijiya da baya a wani hari da aka kai wa ayarinsa .

Rahotanin sun ce lamarin ya faru ne a lokacin wata ziyarar gani da ido da ya kai wani yanki,a karamar hukumar Guma inda ake zargin ana rikici tsakanin manoma da Fulani makiyaya.

Ba dai wanda aka raunata, ballantana asarar rai a farmakin da aka kai wa ayarin gwamnan.

Sai dai rahotanin sun ce an samu asarar rayuka da dama da kuma dukiyoyi a harin da ake kyautata zaton Fulani makiyaya ne suka kaiwa wasu yankuna dake Jihar.