Sabon rikici ya barke a Darfur

Hakkin mallakar hoto d
Image caption 'Yan gudun hijira a Darfur na Sudan

Shugabar hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Navi Pillay ta yi kira a kawo karshen hari a kan fararen hula a yankin Darfur na kasar Sudan ba tare da jinkiri ba.

Arangama ta barke a wani yanki dake El-Geneina babban birnin yammacin Dafur da kuma wani wuri a kusa da Nyala a kudancin Darfur din.

Mutane kimanin miliyan biyu ne suka tagayyara bayan da 'yan tawaye suka shiga gwabza fada da sojojin gwamnati a shekarar 2003.

Masu lura da al'amuran dake faruwa sun ce rikicin baya bayan nan ya kai wani matsayi kwatankwacin yadda ya wakana a farkon tarzomar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sabon rikicin da ya barke a Darfur ya janyo mutane kusan 50,000 sun rasa muhallinsu tun daga watan Fabarairu.

Karin bayani