Isra'ila ta kashe Falasdinawa a Gaza

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Makami mai lunzamin Isra'ila

Wani hari da Isra'ila ta kai da jirgin sama ya hallaka Falasdinawa uku a yankin zirin Gaza.

Kungiyar gwagwarmaya ta Jihad al Islami ta ce wadanda suka rasun mambobinta ne.

Rundunar sojojin Isra'ilar ta ce kai harin ne a gabashin Rafah bayan da aka kaiwa sojojinta hari.

Tun da farko wani jirgin Isra'ilan mara matuki ya fado a daidai wannan wuri.

Sojin sun danganta faduwar jirgin da tangardar na'ura ta kuma ce ta na gudanar da binciken musababbin hadarin.

Isra'ilar dai na amfani ne da jirage marasa matuka wajen tattara bayanan sirri akan yan gwagwarmaya.

Karin bayani