An hana tsohon firai ministan Libya tafiya

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Tun a baya majalisar Libyan ta yi yunkurin cire Ali Zeidan

Mai gabatar da kara na Libya, ya haramta wa hambararren Firai ministan, kasar Ali Zeidan fita zuwa kasashen waje, yayin da ake cigaba da gudanar da bincike a kansa na zargin almundahana.

A ranar Talata ne 'yan majalisar sun ce wani jirgin dakon mai da aka yi wa lodi a wata tashar jiragen ruwa da ke hannun 'yan tawaye, ya sulale daga kofar ragon da sojin ruwan kasar suka yi masa zuwa cikin teku.

Bayan samun rahotannin sulalewar jirgin na Korea ta Arewa, 'yan majalisar suka nemi da a kada kuri'ar yankan kauna akan firai ministan na Libya.

An sayi man da jirgin ya yi dakon nasa ne daga hannun 'yan tawaye da ke iko da tashar jiragen ruwa ta Al-Sidra