Libya ta ce ta tsare jirgin Korea ta Arewa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Babu wata kafa me zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin bangarorin biyu akan jirgin

Gwamnatin Libya ta ce ta kama jirgin ruwan dakon mai me dauke da tutar Korea ta Arewa wanda aka yi wa lodin mai daga wata tashar jiragen ruwa da 'yan tawayen kasar ke rike da ita.

Wani mai magana da yawun kamfanin mai na kasar ya ce, an tsare jirgin a lokacin da yake shirin tafiya, kuma yanzu an tura shi zuwa wata tashar jirgin ruwan da gwamnatin Libyan ke iko da ita.

Fraiministan Libya Ali Zeidan, ya ce, an bayar da umarnin kama wadanda suke cikin jirgin tare da gargadin kasashe da ka da su sayi man.

Sai dai kuma 'yan tawayen sun musanta ikirarin na gwamnati, da cewa har yanzu jirgin yana tsaye a tashar da ke hannunsu ta Al-Sidra.