Jirgin Malaysia:Fasinjoji biyu 'yan Iran ne

Hakkin mallakar hoto Kepolisian Malaysia
Image caption Fasinjoji biyun da ake da shakku a kansu.

Hukumar 'yan sanda ta duniya, Interpol da hukumomin Malaysia, sun yi bayyani a kan wasu pasinjoji biyu da suka yi amfani da fasfunan sata, suka shiga jirgin saman nan da yayi batan-dabo.

In ji Interpol, dukan mutanen biyu 'yan kasar Iran ne, kuma sun yi amfani da fasfunan gaske na Iran din zuwa Malaysia.

Jiragen sama da na ruwa na kasashe dabam-dabam na ta neman jirgin saman da ya bace, kwanaki hudu kenan, amma har yanzu ba a ji duriyarsa ba.

Rundunar soijin sama ta Malaysia ta ce bayanan da aka samu na naurar hangen jirgin sama ya nuna jirgin da ya bace ya karkata akala daga kan hanyarsa ya nufi yamma.

Jirgin Malaysian ya bace ne bayan da ya tashi daga KualaLumpur a kan hanyarsa ta zuwa Beijing kasa da awa guda bayan tashinsa.

Karin bayani