Kwana 4: Ba duriyar jirgin Malaysia

Image caption Hukumomin China sun ce suna son Malaysia ta rika basu bayanai akai akai na halin da ake ciki

Kasar Vietnam ta ce tana fadada aikinta na nemo jirgin saman Malaysian nan da ya bace bat sama ko kasa tsakanin Kuala Lumpur da Beijin ranar Asabar.

Gwamnatin kasar ta ce tana tura karin jiragen ruwa da na sama, domin su shiga aikin laluben a gabar tekunta.

Kasashe tara ne ke aikin neman gano tarkacen jirgin, da har yanzu ba a ga wata alamarsu ba.

Mutane 239 ne a cikin jirgin da ya bace ba tare da wata alama ta neman agaji ba.

Su kuwa hukumomin kasar China da yan kasar suka fi yawa cikin jirgin sun bukaci Malaysia ta kara azama wajen neman jirgin.

Karin bayani