Shehun Borno ya umurci a yi azumi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi

Basaraken gargajiya a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nigeria, Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, ya umarci al'ummomin jihar su yi azumi na kwanaki uku daga ranar Talata don Allah Ya kawo dawwamammen zaman lafiya a yankin.

Jihar ta Borno ta kasance matattarar 'yan kungiyar Boko Haram, inda hare-harensu ya janyo mutuwar dubban mutane a cikin jihar da kuma wasu jihohin arewacin kasar.

Manufar yin azzumin da kuma gudanar da addu'o'i shi ne don rokon Allah ya kawo karshen zubar da jinin da ake yi a yankin.

Rahotanni sun al'ummomin Musulmi da Krista a jahar Borno sun tashi da azumin a ranar Talata.

Tun daga farkon wannan shekarar da 'yan Boko Haram sun kaddamar da munanan hare-hare lamarin da ya janyo hasarar dinbim rayuka ciki hadda na matasa da mata da kananan yara tare da barnata dukiyoyin jama'a.

A halin yanzu dai dubban mutane ne a jihar ta Borno suka fice daga muhallansu suka tsallaka makwabtan jihohi saboda hare-haren 'yan Boko Haram.

Watanni goman da suka wuce ne ake amfani da dokar ta-baci a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa, masu fama da hare-haren da ake dangantawa da 'yan Boko Haram.

Karin bayani