'Yan sandan Afrika ta Kudu sun doki dan Nigeria

Dan kasar Mozambique da aka kashe a Afrika ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan kasar Mozambique da aka kashe a Afrika ta Kudu

An kama wasu jamian 'yan sanda biyu na kasar Afrika ta kudu bayan wani hoton bidiyo da aka saka a shafin internet ya nuna lokacinda suke cire tufafin wani dan Najeriya tare kuma da lakada masa duka akan titi.

Bidiyon ya nuna yadda 'yan sanda a garin Cape town suka rika lakadawa mutumin duka.

Kakakin rundunar 'yan sanda ya ce lamarin ya tayar masa da hankali.

A bara ne dai aka hukunta wasu 'yan sanda tara bisa zargin kashe wani dan kasar Mozambique direban taxi wanda wata motar yan sanda ta rika ja a kasa.